Yayin ganawar tasu, shugaba Kenyatta ya ce, kasarsa na ba huldar dake tsakanin kasashen 2 muhimmanci matuka, kuma har kullum kasarsa ta Kenya tana tsayawa tsayin daka kan manufar "Kasar Sin daya tak a duniya", tare da nuna cikakken goyon baya ga shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin.
Haka zalika, shugaban ya ce Kenya na son zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin 2 musamman ma a fannin aikin tsaron kasa, don tabbatar da moriyar jama'ar kasashen 2.
A nasa bangare, Chang Wanquan ya ambato ziyarar da shugaba Kenyatta ya kawo kasar Sin a watan Mayun bana don halartar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", inda shugaban ya gana da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, inda suka cimma matsayar daga huldar dake tsakanin kasashen 2, zuwa ta kawayen dake hadin kai bisa manyan tsare tsare a dukkan fannoni.
A cewar jami'in, makasudin tafiyarsa kasar Kenya a wannan karo shi ne, aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, tare da sa kaimi ga zurfafa huldar dake tsakanin sojojinsu.(Bello Wang)