Sakatariyar gwamnatin kasar Kenya Amina Mohamed, wadda ta bayyana haka yayin taron gama gari na AU karo na 29, ta ce Tarayyar ta samar da wasu tsare-tsare kan irin rawar da yawan jama'a masu jini a jika za su iya takawa wajen raya kasashensu, wanda ake sa ran kasashe mambobin za su aiwatar.
Cikin wata sanarwar da sakatariyar ta fitar gabanin babban taron AU inda za ta wakilci shugaba Uhuru Kenyatta, ta ce tsare-tsaren za su mai da hankali kan wasu muhimman batutuwa 4 da suka hada da kiwon lafiya da kyautata zaman rayuwa da ilimi da koyar da fasahohi, sai aikin yi da sana'a da kuma shugabanci.
Ta ce ana sa ran taron na gama gari mai taken "amfani da gudumuwar da jama'a za su iya bayarwa ta hanyar karfafawa matasa", zai zaburar da shugabannin Afrika da dukkan masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su karfafawa matasa a Afrika. (Fa'iza Mustapha)