Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu an sayar da kimanin tikiti 14,000 kuma daga cikin wannan adadi 2,000 ne kawai fasinjoji suka saya, ciki har da ma'aikatan dake aikin gina layin dogon da mazauna wurin a matsayin kyauta ga 'yan uwa da abokai domin murnar kaddamar da layin dogon.
Babban manajan dake kula da layin dogon Huang Jincan ya shaidawa taron manema labarai cewa, tun a ranar 4 ga watan Yunin wannan shekara ce aka kammala sayar da bakin dayan tikicin jirgin da zai tashi daga Mobasa zuwa Nairobi, inda daruruwan fasinjoji dake ciki suka bayyana cewa,ba su samu tikitin a wannan rana ba.
Ya ce, daga ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara za a kara lokutan da jirgin yake zirgz-zirga saboda yawan bukatar tikitin. Inda ake sa ran jirgin zai rika kai koma tsakanin tashoshin dake biranen biyu a kowace rana.
A halin yanzu dai layin dogon mai nisan kilomita 489 da aka kaddamar a ranar 1 ga watan Yunin, yana zirga-zirga ne tsakanin Nairobi da Mombasa a kowace rana.(Ibrahim)