Shugaban rundunar 'yan sandan yankin dake gabar teku Phillip Tuimur ya bayyana cewa, yanzu 'yan sandan suna gudanar da bincike a wurin da harin ya auku, an kuma tura karin ma'aikata domin kwashe wadanda suka ji rauni.
Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin kai harin, amma galibin hare-haren da ake kaiwa a yankin dake tsakanin kasar Kenya da Somaliya kwanan baya, suna da alaka da kungiyar Al-Shabaab.
Kungiyar Al-Shabaab dai wani reshe ne na kungiyar al-Qaeda dake kasar Somaliya, kuma a shekarun baya bayan nan, kungiyar Al-Shabaab ta yi ta kai hare-hare a kasar Somaliya da wasu kasashen dake makwabtaka da ita. (Maryam)