in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A shirye kasar Sin take ta fadada dangantaka da Ghana ta yadda za su mori juna
2017-07-01 09:53:53 cri
Jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohang, ta ce a shirye Gwamnatin kasar Sin ta ke ta fadada dangantakar moriyar juna tsakaninta da Ghana.

Da take amsa tambayoyin manema labarai bayan bada gudunmuwar kayayyakin samar da lantarki daga hasken rana da darajarsu ta kai miliyoyin daloli ga gwamnatin Ghana, jakadar ta yi bayanin cewa, duk abun da kasashen biyu za su yi, za su yi shi ne ta yadda za su mori juna.

Ta kuma bayyana ziyarar da Mataimakin Shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia ya kawo kasar Sin a baya-bayan nan a matsayin wanda mai dimbin nasara, ta na mai cewa ziyarar ta jadadda yadda Ghana ta dauki dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin da muhimmanci.

Jakadar ta kara da cewa, ziyarar babbar alama ce dake nuna cewa Ghana na son karfafa huldar dake tsakaninta da kasar Sin ta fuskar moriyar juna.

Da take tsokaci kan baki dayan dangatakar dake tsakanin kasashen biyu, Sun Baohang, ta bayyana gamsuwa game da yadda cinikayya tsakanin kasashen ta habaka, daga dala miliyan 100 a shekarar 2000, zuwa dala biliyan 6.6 a shekarar 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China