in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na taimakawa ci gaban Afirka
2017-07-05 10:02:38 cri
Jakadar kasar Sin dake kasar Ghana Sun Baohong ta bayyana kudurin kasarsa na taimakawa kasashen Afirka su raya kansu bisa tafarkin da ya dace da su.

Jakada Sun ta bayyana hakan ne yayin ganawar kwararru kan raya nahiyar Afirka a yayin bude taron hadin gwiwar Sin da Afirka dangane da bincike da musayar shirye-shirye tsakanin kasashen biyu.

Jami'ar ta ce kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki ta yanar gizo, musayar muhimman bayanai, makamashin da ake sabuntawa, da kuma kare muhalli. Haka kuma kasar Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka, ko tilasta musu yin wani abu ba. Kana ba ta da wata manufa ta boye a duk wata huldar dake tsakaninta da kasashen nahiyar.

A jawabinsa na bude taron, mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamadu Bawumia, ya yabawa kasar Sin kan irin rawar da take takawa a kasashen Afirka. Yana mai cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka ya dace da muradun nahiyar na fitar da al'ummominta daga kangin talauci.

Ana sa ran taron na kwanaki biyu wanda cibiyar wanzar da tsarin demokuradiya (IDEG) ta shirya zai tattauna kan yadda kasashen Sin da Afirka za su hada kai a fannonin kwararru da fasahohi don raya nahiyar da kuma yin hadin gwiwar moriyar juna. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China