in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Ghana ya karu zuwa kashi 6.6 cikin dari cikin watanni ukun farkon shekarar nan
2017-06-29 13:40:08 cri
Hukumar kiddidiga ta kasar Ghana, ta ce alkaluman GDP na kasar, wanda ma'uni ne na habakar tattalin arziki, ya kai kashi 6.6 cikin watanni ukun farkon shekarar nan.

Mataimakin babban jami'in hukumkar, Anthony Amuzu wanda ya sanar da haka a jiya, ya ce cikin makamancin lokacin a bara, alkaluman sun nuna cewa tattalin arzikin ya tsaya ne a kashi 4.4, a lokacin da aka samu matsalar makamashi da ta kai ga karancin samar da man fetur, al'amarin da suka yi wa tattalin arzikin kasar illa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China