Yankin dake da albarkatun man wato (OCTP), ya kunshi yankin da ake saran samar da man wanda ya kai ganga 45,000 a kowace rana, da kuma iskar gas wanda ya kai cubic mita miliyan 171 a kullum wanda ake saran fara aikinsa a shekarar 2018.
Shugaban na Ghana ya ce, abokan hulda masu zuba jari sun nuna sha'awarsu na gudanar da aikin duk da rashin tabbas din da ake da shi sakamakon karyewar farashin danyen man a kasuwannin duniya.
Akufo-Addo ya ce suna cigaban da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da ganin kasar Ghana ta zama babbar cibiyar samar da man fetur a yammacin Afrika. (Ahmad)