Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ya bukaci sojojin kasar da su kara azama domin kawo karshen harin mayakan Boko Haram wanda ya jima yana ta'azzara al'amurra a yankin.
Shettima ya yi wannan roko ne a lokacin da yake gabatar da jawabin murnar bikin karamar salla ta bana a Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce, ko da yake sojojin Najeriyar sun samu gagarumar nasara a kan mayakan, sai dai yawan hare haren da Boko Haram ke kaddamarwa a sassa daban daban na jihar a yan kwanakin nan sun kasance abu ne mai tayar da hankali.
Kashim Shettima ya ce, ya zama tilas a yabawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dakarun sojin kasar sakamakon kokarin da suka yi wajen yakar mayakan na Boko Haram a shiyyar.
Sai dai a cewar gwamnan, makonni biyu da suka gabata, an fuskanci manyan kalubaloli masu yawa a garuruwan Damboa, Chibok, da kuma birnin Maiduguri da kewaye dake jihar.(Ahmad Fagam)