in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram 700 sun mika wuya
2017-07-04 10:17:09 cri
Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Litinin cewa, kimanin mayakan Boko Haram 700 ne suka mika wuya a jahar Borno.

Babban hafsan sojin kasar Tukur Buratai shi ne ya ya tabbatar da hakan a lokacin gudanar da bikin ranar sojoji na tsawon mako guda inda dakarun Najeriyar suka ayyana muhimman nasarorin da suka cimma a fafutukar da suke yi na murkushe ayyukan ta da kayar baya a kasar.

Ya ce wasu da dama daga cikin mayakan sun mika wuya, wannan ya bayyana a fili cewa dakarun Najeriyar sun karya lagon mayakan Boko Haram a yakin da suke yi da 'ya'yan kungiyar.

Ya ce wannan babbar nasara ce, kasancewar mayakan 'yan ta'addan sun riga sun yanke shawarar mika wuya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China