Gwamnan Jihar Lagos kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya Akinwunmi Ambode, ya ce Gwamnati na daukar matakan gaggawa na lalubo mafita game da matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
Da yake jawabi yayin wani taron wayar da kai game da fasahohin da suka danganci samar da ruwa da kula da muhalli da ya gudana jiya a Lagos, Gwamnan ya ce akwai bukatar gaggawa na nazari tare da sake fasalta hanyoyin ruwa da kwalbatoci a jihar.
Akinwumi Ambode ya shaidawa mahalarta taron cewa, Gwamnati za ta kara kaimi wajen kafa dokokin tsarin gine-gine, musammam wadanda suka shafi gini ba bisa ka'ida ba a kan hanyoyin ruwa, lamarin dake toshe gudanar ruwa yadda ya kamata a fadin jihar.
Ya ce Gwamnatinsa za ta sake farfado da gangaminta na yaki da zubar da shara da jama'a ke yi a magudanar ruwa.
Akinwumi Ambode ya kara da cewa, kula da hanyoyin albarkatun ruwa da muhalli na ci gaba da zama babban kalubale da sassan duniya masu tasowa ke fuskanta. (Fa'iza Mustapha)