in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulki a Nijeriya ta ce shugaban kasar dake jinya na samun sauki
2017-07-01 10:06:36 cri
Jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya, ta ce shugaban Kasar Muhammadu Buhari dake jinya a wani asibiti a birnin London na samun sauki sosai, sabanin rade-raden da ake yadawa cewa, rayuwarsa ta dogara ne akan injuna.

Sai dai Shugabancin Jam'iyyar ya ce likitocin nasa dake kasashen waje ne kadai za su iya fadin lokacin da zai koma gida.

Da yake ganawa da manema labarai a jiya, shugaban Jam'iyyar APC na kasa John Odigie-Oyegun, ya ce jam'iyyar na farin cikin sanar da cewa, Shugaba Buhari na samun sauki cikin sauri, inda ya ce suna da yakinin idan ya dawo, babu tantanma za a shiga wani sabon babi na gudanar da ayyuka.

A ranar Laraba da ta gabata ne, Gwamnan jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Kasar Ayodele Fayose, ya fara yada jita-jitar cewa shugaban baya cikin hayyacinsa inda rayuwarsa ta dogara kan injina a asibitin da yake jinya a London.

A ranar 7 ga watan Mayu ne shugaban kasar mai shekaru 74 ya tafi asibitin, kusan watanni biyu bayan ya koma gida daga jinya da ya yi a birnin na London. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China