in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen saman Ethiopia zai sauka jiragensa a birnin Kadunan Nijeriya
2017-07-07 08:51:25 cri

Kamfanin jiragen saman Ethiopia, ya ce ya kammala shirye-shiryensa na fara jigila sau uku cikin kowane mako a birnin Kadunan Nijeriya daga ranar 1 ga watan Augusta.

Wata sanarwar da kamfanin ya fitar, ta ce Kaduna wanda ke arewa maso yammacin Nijeriya, babbar cibiya ce ta cinikayya da sufurin albarkatun gona daga yankunan dake kewaye da ita, la'akari da layin dogo da kuma hadakar tituna da take da su.

Shugaban kamfanin Tewolde Gebre Mariam ya ce kamfanin zai ci gaba da fadada harkokinsa a cikin nahiyar Afrika.

A cewar sanarwar, da karin da aka samu na Kaduna, jiragen Ethiopian za su rika jigila sau 23 cikin kowane mako a Nijeriya, a biranen da suka hada da Abuja da Lagos da Enugu da Kano, kuma da Kaduna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China