Kwayoyin cuta ne ke haddasawa tare da yada murar wadda ba ta daukar lokaci mai tsawo, a tsakanin tumakai da raguna da awaki, inda suke kamuwa da zazzabi da yoyon hanci da tari da kuma limonia, a wasu lokuta ma ya kan kai ga mutuwa.
Darakta a ma'aikatar harkokin gona da raya karkara na kasar Gideon Mshelbwala ne ya bayyana haka jiya Talata a Abuja, fadar mulkin kasar.
Gideon Mshelbwala, ya kuma tabbatarwa al'ummar kasar kudurin gwamnati na tabbatar da yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)