Cikin wata sanarwar da aka fitar jiya Laraba, Mansur Dan-Ali, ya ce daga cikin yunkurin fashi 16 da aka yi cikin wannan lokaci, 4 kawai aka yi nasarar yi.
Ya ce cikin makamancin wannan lokaci a bara, 36 daga cikin hare-hare 55 da aka yi niyyar kaiwa, sun cimma nasara.
A cewarsa, a shekarun baya-bayan nan, kiraye-kirayen ballewa da ake a yankin Niger Delta na kasar, sun taimaka wajen kara kai hare-hare kan bututu da jiragen dakon mai, baya ga satar mutane don neman kudin fansa, da fasa bututun danyen man fetur tare da tacewa a haramtattun matatu don sayarwa ga kasashen waje da ake yi.
Ministan ya kara da cewa, shirye-shiryen inganta ababen more rayuwa da tattaunawa da ake yi da al'ummomi, da kuma dorewar shirin yafiya ga tsageru da kuma inganta harkokin cikin ruwa, sun taimaka sosai wajen bunkasa tsaro a gabobin ruwan Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)