in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu za ta inganta sa ido a iyakokinta saboda fargabar yaduwar cutar Ebola
2017-05-26 09:52:01 cri
Sudan ta kudu za ta inganta matakan sa ido a iyakarta da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, domin kare yaduwar cutar Ebola mai saurin kisa.

Mataimakin sakatare a ma'aikatar lafiya ta kasar Makur Koriom, ya ce za a tura tawagar jami'an lafiya zuwa yankunan da ke kan iyakar kasar da Jamuriyar Demokradiyyar Congo, domin sanya ido da ilmantar da al'ummomi dake jihar Equatoria dake yammacin kasar, game da matakan kiwon lafiya.

A karshen watan Afrilun da ya gabata ne, Hukumar lafiya ta duniya ta bada rahoton samun bullar cutar Ebola a lardin Bas Uele dake arewacin Demokraddiyar Congo, inda ake zaton mutane 29 sun kamu da cutar sannan wasu uku sun mutu a sanadinta.

Barkewar cutar ta jefa fargaba a zukatan al'ummomin Sudan ta Kudu wadanda ke zaune a yankunan dake dab da iyakar kasar da Jamhuriyar Demokraddiyar Congo.

Makur Korium ya ce abu na farko da aka sanya a gaba shi ne, kore fargaba daga zukatan al'umma tare da wayar musu da kai game da ilollin dake tattare da cin naman daji na dabobbi kamar biri, wanda ake tsammanin na dauke da kwayar cutar Ebola.

Ya kuma musanta rahoton dake cewa, Sudan ta Kudun ta rufe iyakarta da Jamhuriyar Demokraddiyar Congo, ya na mai cewa, hadarin yaduwar cutar zuwa kasar ba shi da yawa, la'akari da nisan dake tsakanin kasar da yankunan da abun ya shafa da kuma matakan da Jamhuriyar Demokraddiyar Congon ta dauka na yaki da cutar.

An samu barkewar cutar Ebola a Sudan ta Kudu a shekarar 2004 a yankin Yambio dake kan iyakar kasar da Jamhuriyar Demokraddiyar Congo, inda hukumar WHO ta bada rahoton cewa, mutane 20 ne suka kamu da cutar, ciki har da 5 da suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China