Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin fadar shugaban Najeriya Laolu Akande ta bayyana cewa, yayin ganawar shugabannin biyu sun tabo irin gagarumar rawar da kasashen biyu suka taka a yankin yammacin Afirka, batun taron kolin kungiyar AU dake tafe a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, da yarjejeniyar cinikayyar nahiyar da ake tattaunawa a kai, da kuma yadda za a farfado da hukumar hadin gwiwa ta din-din-din tsakanin kasashen biyu.
Bugu da kari, shugabannin sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwar da za ta taimakawa ci gaban shiyyar.
Shugaba Akufo Addo ya ce ziyarar da ya kawo Najeriya wani bangare ne na rangadin da yake gudanarwa a shiyyar don sanin irin abubuwa dake faruwa a shiyyar baki daya tare da sake sabunta dangantaka tsakanin kasashen da ke shiyyar. Ya kuma yi fatan shugabanin kasashen yankin na ECOWAS za su hada kai ta yadda haka za ta cimma ruwa.(Ibrahim)