Shugaban sashen bunkasa jagorancin jam'iyyar Fikile Mbalula ne ya bayyana hakan a birnin Johannesburg a jiya Lahadi, yana mai cewa ANC na fatan zabar gogaggun jagorori masu da'a, da sanin makamar aiki, wadanda za su iya jagorantar ta, da kuma jama'ar kasar baki daya.
Mr. Mbalula ya kara da cewa, jam'iyyar ta bullo da tsari na ilmantar da 'ya'yanta, ta hanyar tura manyan jami'anta zuwa kasar Sin da nufin samun karin horo. Kazalika ana daukar matakai na rage mambobin kwamitin zartaswa. Ya ce kafin hakan, a halin da ake ciki ANC na da mambobi da yawansu ya kai mutum 86 a kwanitin ta na zartaswa.
Fikile Mbalula ya ce "muna fatan koyi da tsarin kwamitin koli na JKS wato CPC, wanda ke da mambobinsa na kwamitin zartaswa da ba su wuce 25 ba. Ya ce wadannan mambobi ba wai kawai na jeka-na-yika ba ne, a'a suna da kwarewa matuka wajen gudanar da aikin da aka dora masu, domin kuwa sun samu horo na ayyukan samar da ci gaba, sun kuma fahimci jam'iyyar kwarai da gaske. (Saminu Hassan)