ANC ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bisa ga yadda aka auna matsayin da kasar Afrika ta kudun za ta biya basusukan dake kanta, hakan ba yana nufin zai illata yanayin tattalin arzikin kasar ba ne.
Ita dai kasar ta Afrika ta kudu ta gamu da koma bayan ne bisa matsayin basusukan da hukumomin kiddidigar kudade na kasa da kasa suka bayar game da matsayin basusukan da ake bin kasar a ranakun 3 da kuma 7 ga wannan wata na Afrilu.
Dukkannin hukumomin kudin sun yi amana cewa matsalar dambarwar siyasa shi ne ummul-aba-isin da ya haddasa wannan matsalar koma bayan.
ANC ta ce tabarbarewar yanayin basusukan kasar zai iya zama babban koma baya ga kasar wajen samun rancen kudaden gudanar da ayyukan raya kasa, musamman a yayin da ake ciki na samun koma baya ga kudaden tsimi na cikin gidan kasar. (Ahmad Fagam)