An ba tawagar lambar yabon ne yayin wani bikin da ya samu halartar jami'an Gwamnatin Zambia da na ofishin jakadancin Sin dake kasar.
Kakakin Ma'aikatar lafiya na Zambia Kennedy Malama, ya ce tawagar likitocin ta kasance a kasar cikin shekara daya da ta gabata, kuma ta taka rawar gani da ba za a manta da ita ba, saboda jajircewar likitocin a kan aiki.
Ya ce likitocin Zambia sun koyi abubuwa da dama daga tawagar likitocin da ta aiwatar da ayyukanta ba tare da wata matsala ba, inda likitocin suka rika musayar ilimi da likitocin kasar Zambia.
A nasa bangare, mai kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin Chen Shijie, ya ce ba kadai fasahohin kiwon lafiya na zamani tawagar ta kai kasar ba, har ma da magunguna da wasu dabarun kiwon lafiya na gargajiya na kasar Sin.
Ya kara da cewa, sun kuma taimaka wajen horar da likitocin na Zambia, ta hanyar koyar da su yadda ake amfani da sabbin fasahohi.
Chen Shijie, ya ce tun daga shekarar 1978 zuwa yanzu, kasar Sin ta aike da likitoci 487 zuwa Zambia. (Fa'iza Mustapha)