A cewar jadawalin da ofishin majalisar ta wallafa, kasar Sin za ta inganta ayyukan masana'antu da inganta muhalli da hada kan kabilu da kuma kara inganta tsaron kasa a yankunan kan iyaka.
Jadawalin ya ce la'akari da budewar kofofin kasar, inganta tsaron iyakoki da tsaron muhallin hallitu a yankunan kan iyaka na da mutukar muhimmanci ga manufofin kasar na samar da ci gaba.
Har ila yau, ya bayyana cewa, raya yankunan kan iyaka zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba a fannin zamantakewa da tattalin arziki, da walwalar mazauna yankunan da hadin kan kasa tare da samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin kasar Sin da sauran kasashe. (Fa'iza Mustapha)