Mataimakin shugaban bankin Bao Jian'an, ya shaidawa wani taro da aka yi jiya Talata kan rage fatara cewa, za a samar da rancen ne ga manyan masu ayyukan gona da masana'antu na musamman.
Domin kawar da fatara zuwa karshen 2020, dole ne kasar Sin ta fitar da mutane miliyan goma daga kangin talauci a kowace shekara ta hanyar samar da masana'antu da sauya wuraren aiki da kuma shirye-shiryen kula da al'umma.
Bankin ADBC ya ce rancen na rage radadin talauci ba zai gaza kashi 60 na jimilar basussukansa ba. Zuwa karshen shekarar 2016, basussukan da ake bi sun kai Yuan biliyan 901
Bankin wanda aka kafa a shekarar 1994 na da alhakin samar da kudadedn gudanar da ayyuka da suka shafi harkokin noma da samar da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)