Cikin sanarwar da kakakinsa Stephane Dujjaric ya fitar a jiya, Antonio Guterres ya aike da sakon jaje ga al'umma da gwamnatin Nijeriya, inda ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa tare da fatan za a tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu wajen kai harin.
Sakatare Janar din ya jadadda goyon bayan MDD ga gwamnatin Nijeriya a yaki da take da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi.
Rahotanni sun ce 'yan kunar bakin wake sun kai hare-haren bama bamai kan birnin Maiduguri, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu 13. (Fa'iza Mustapha)