in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Ghana ta dukufa don ganin ta hana yara watangarari a tituna.
2017-06-17 12:41:04 cri

Ministar kula da Jinsi da yara da kuma kare al'umma ta kasar Ghana Otiko Afisah Djaba, ta bayyana damuwa game da karuwar adadin yara dake watangarari a titunan kasar.

Da take jawabi yayin wani taro domin ranar yaran nahiyar Afrika, ta ce al'amarin na nuni da cewa Ghana na da jan aiki a gaban ta na magance wannan kalubale.

Otiko Afisah ta ce abun damuwa ne ganin yara suna bara da sayar da abubuwa da kuma wanke gilasan mota a kan tituna, ta na mai cewa, ma'aikatarta za ta gano tare da tattara bayanan wadanan yara.

Har ila yau, Ministar ta ce ma'aikatar ta daura damarar yaki da safarar yara, kuma ta na aiki da hukumomin a jihohi da ma'aikatu da masu ruwa da tsaki, don ganin an gurfanar da masu aikata laifin.

Kasashe Mambobin Tarayyar Afrika ne ke bikin ranar yaran Afrika a ranar 16 ga watan Yunin ko wacce shekara, domin tunawa da rikicin Soweto na kasar Afrika ta kudu na shekarar 1976. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China