Wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya, ta ruwaito Nana Akufo-Addo na cewa, idan aka ba matasa damar da suke bukata, to za a samu gagarumin ci gaba ta fuskar tattalin arziki cikin kankanin lokaci.
Da yake jawabi ga taron kawancen kungiyar G20 da Afrika dake gudana a Berlin na kasar Jamus, shugaban kasar ta Ghana, ya ce idan aka samar da yanayi mai kyau a Afrika, wanda zai ba matasa damar inganta kwarewarsu, aka kuma horar da su sana'o'in hannu tare da samun ilimin fasahar zamani, to za su bunkasa nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)