in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya nemi a dauki makatan dakile ta'ammali da kudaden haram a Afrika
2017-07-02 13:19:08 cri

Jami'in hukumar kula da tattalin arziki na MDD game da kasashen Afrika (UNECA), ya bukaci a kara daukar matakan da za su dakile ta'ammali da kuddaden haram a Afrika, wanda aka kiyasa yawan da ake samu a duk shekara ya kai dala biliyan 80.

A lokacin da yake yin tsokaci a taron koli na AU karo 29 tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yulin a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, Abdalla Hamdok, mai rikon mukamin babban sakataren UNECA, ya bayyana cewa, dakile ta'ammali da kudaden haram a nahiyar Afrika al'amari ne mai matukar muhimmanci, musamman wajen samun nasarar aiwatar da shirin nan na ajandar dauwamammen cigaba nan shekarar 2030 da kuma 2063.

Ya ce bisa la'akari da irin mummunan tasiri da wannan matsala ke haifarwa wajen mayar da hannun agogo baya game da ciagaban Afrika da koma bayan da ake samu game da ajandojin cigaban gwamnatocin Afrika, batun karuwar halasta kudaden haram za'a iya cewa wannan matsala ba ta tsaya iya Afrika kadai ba har ma ta shafi duniya ne baki daya.

Hamdok, ya jaddada bukatar daukar kwararan matakan dakile wannan matsalar yaduwar ayyukan halasta kudaden haram a nahiyar ta Afrika.

Ya ce a halin yanzu an kaddamar da hadin gwiwa tsakanin manyan kungiyoyin Afrika, kana hadin gwiwar hukumar UNECA da AU zai taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar dakile matsalar.

Jami'in na UNECA ya nemi a shawo kan matsalar bakin haure a Afrika, inda ya bayyana matakin da cewa zai taimaka wajen rage talauci, da samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arziki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China