in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna maraba kan Liberia da ta karbi aikin tsaro daga hannun MDD
2016-07-01 10:18:24 cri
Jiya Alhamis 30 ga watan Yuni, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya fidda wata sanarwar ta bakin kakakinsa cewa, ya yi murna sosai ganin gwamnatin kasar Liberia ta karbi dukkan ayyukan kiyaye tsaron kasa daga hannu tawagar musamman ta kiyaye zaman lafiya da MDD ta tura wa kasar.

Cikin wannan sanarwa, Ban Ki-moon ya nuna girmamawa matuka ga gwamnati da al'ummomin kasar Liberia dangane da kokarin da suka yi wajen kiyaye zaman lafiyar kasa bayan da aka kawo karshen rikicin kasar a shekarar 2003, lamarin da ya tabbatar da zaman karko a kasar, shi ya sa, a halin yanzu, MDD za ta daukar matakinta na karshe wajen kiyaye zaman lafiya a wannan kasa.

Ban Ki-moon ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa a kasar Liberia da su ci gaba da karfafa zaman lafiya, tare da mika aikin kiyaye tsaron kasa da aka yi shaida babban sakamakon da aka cimma wajen tabbatar da yunkurin zaman lafiya a kasar, lamarin da ya nuna amincewarmu matuka kan kokarin da al'ummomin Liberia suka bayar wajen gina wata kasa mai cike da zaman lafiya, da zaman karko, haka kuma za ta kasance wata kasa dake kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata, yayin da take gudanar da ayyukanta bisa dokoki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China