in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na kokarin sasanta rikicin siyasar DR Congo da Gabon
2017-07-02 12:25:50 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta fara tattaunawar shiga tsakani da nufin warware rikicin zabuka a Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo (DR Congo) da kasar Gabon.

Da take zantawa da manema labarai a lokacin taron kolin AU karo na 29 wanda ke gudana tsakanin ranakun 27 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yuli a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, Minata Samate Cessouma, kwamishinar AU mai kula da al'amurran siyasa, ta bayyana cewa, warware dambarwar siyasar zai taimaka wajen inganta rayuwar matasan nahiyar Afrika.

DR Congo ta sha fama da matsalolin rikicin siyasa da na mulkin soji, lamarin da ya haddasa jan kafa wajen gudanar da zaben shugaban kasar wanda da farko aka shirya gudanarwa tun a shekarar 2016 da nufin sauya gwamnatin shugaban kasar mai ci Joseph Kabila.

Haka zalika, an sanya ranar 29 ga watan nan na Yuli don gudanar da zaben shugaban kasar Gabon, sai dai abokan takarar shugaban kasar mai ci Ali Bongo, suna zargin gwamnatinsa da yunkurin shirya magudin zabe.

Rikicin zaben wanda ya rikide ya koma tashin hankali, ya tilastawa wasu 'yan kasar musamman mata da kananan yara yin gudun hijira, inji Cessouma.

Khabele Matlosa, daraktan sashen al'amuran siyasa na AU ya bayyana cewa, muddin ana son kaucewa tashe-tashen hankula, tilas ne hukumomin da aka dorawa alhakin gudanar da zabuka a kasar su tsaya tsayin daka don yi aiki tukuru bisa gaskiya da rikon amana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China