Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar Tony Opuiyo ya fitar, ta ce an kame mutanen ne a jihar Sokoto dake yankin arewa maso yammacin kasar.
A cewar hukumar, manufarsu ita ce, shirya jerin hare-hare da ababen fashewa a garuruwa daban-daban na kasar dake yankin yammacin Afrika, musammam lokacin bukukuwan karamar sallah.
Hukumar ta kara da cewa, kungiyar ta shirya kai hare-hare wuraren taron jama'a kamar kasuwanni da wajen shakatawa da na bude ido da wajen ibadu, musammam masallatan idi da sauran wuraren dandazon jama'a yayin bukukuwan na sallah.
Gwamnatin Nijeriya dai ta samu gagarumar nasara a yaki da take da kungiyar ta Boko Haram, inda dakarunta suka fatattaki mayakanta daga tungarsu dake dajin Sambisa cikin watan Janairun da ya gabata.
A kalla mutane 1,400 da ake zargin 'ya'yan kungiyar ne a yanzu haka ke tsare hannun hukumomin tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar. (Fa'iza Mustapha)