in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya alkawarta ci gaba da tallafawa yankin Hong Kong
2017-06-29 13:42:27 cri

Shugaban kasar Xi Jinping, ya ce gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa yankin Hong Kong mai cin gashin kan sa, a fannin bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar sa.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, jim kadan bayan saukar sa a filin jirgin sama na kasa da kasa dake Hong Kong. Shugaban na Sin zai gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki 3 a yankin, zai kuma halarci bikin cika shekaru 20 na komawar yankin Hong Kong din bangaren kasar Sin.

Kaza lika zai halarci bikin kaddamar da gwamnatin yankin ta biyar, da kuma gudanar da ziyarar aiki a wasu sassan yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China