in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon taya murnar kaddamar da taron koli na 29 na AU
2017-07-03 18:09:55 cri

A yau Litinin 3 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga al'ummar Afirka game da bude taron koli na 29 na kungiyar tarayyar Afirka AU, wanda ke gudana a Addis Ababa na kasar Habasha.

Cikin sakon, Shugaba Xi ya nuna cewa, AU na dukufa kan aikin dunkulewar kasashen Afirka gu daya, da sa kaimi ga samun damar yin magana da murya guda a kan muhimman lamuran duniya da na shiyya-shiyya, kuma ta samu kyawawan sakamako a wadannan fannoni. Xi kuma ya nuna fatansa, na ganin yadda AU za ta shugabanci kasashen Afirka, wajen samun manyan nasarori a sha'anin neman samun zaman lafiya da ci gabansu.

Haka kuma Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kara azama ga aiwatar da manyan shirye-shiryen nan goma na hadin kan Sin da Afirka, da shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin su dace da Ajandar AU ta shekarar 2063, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar hadin gwiwar Sin da Afirka daga dukkan fannoni zuwa gaba, gami da amfanar jama'ar bangarorin biyu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China