in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan Jami'an Afrika za su gana gabanin babban taron AU karo na 29
2017-07-01 10:41:07 cri
An kaddamar da taron gama gari na 31 na majalisar Zartawar Tarayyar Afrika AU a jiya Juma'a, a wani bangare na tsare-tsaren babban taron Tarayya karo na 29 da za a yi a Addis Ababa babban birnin Habasha.

Yayin taron na yini biyu, ministocin harkokin wajen kasashe mambobin AU, za su tattauna kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro da sake fasalin tarayya da kuma batun kaura.

A jawabinsa yayin bude taron, Shugaban Hukumar kula da AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa, zaman lafiya da tsaro na daya daga cikin manyan batutuwa da aka sanya gaba, inda ya ce ana bukatar sabbin dabarun tunkarar sabon salon nau'ikan rikice-rikice dake aukuwa a nahiyar.

Ya ce babu wani tashin hankali a Afrika da za a iya warwarewa ta hanyar amfani da makami, ya na mai jaddada bukatar hawa teburin sulhu da tattaunawa da kuma lalubo hanyoyin cimma mafita guda na warware matsalolin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China