Ramaphosa yace wannan rahoto karya ce tsagwaronsa wanda ake yadawa, inda a cewarsa mutane suna yada jita jita ne cewa wai ya ajiye aikinsa ne sakamakon nuna turjiya game da matakin da shugaba Jacob Zuma ya dauka na yin garambawul a majalisar ministocin kasar tun da sanyin safiyar Juma'ar data gabata.
Ramaphosa yace hakika da farko ya nuna rashin jin dadi game da matakin da shugaba Zuma ya dauka na yin garambawul a majalsar ministocin kasar, musamman ya kalubalanci mai gidan nasa saboda tunbuke ministan kudin kasar Pravin Gordhan daga mukaminsa.
Dama dai, tun gabanin shugaban kasar Afrika ta kudu ya dauki wannan mataki na yiwa majalisar ministoci gyaran fuska, wanda ya shafi ministoci 10 da mataimakan ministoci 10, sai da Zuma ya gana da manyan shugabannin jamiyyarsa ta ANC, amma a cewar mista Ramaphosa, kawai ya sanar da kusoshin jam'iyyar ne game da matakin da yake son dauka.
Mai magana da yawun mataimakin shuagban kasar Ronnie Mamoepa, ya tabbatar a jiya Asabar cewe, har yanzu Ramaphosa yana kan kujerarsa ta mataimakin shugabann kasar, kuma mataimakin shugaban jamiyyar ta ANC.