in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kaddamar da layin dogo daga Mombasa zuwa Nairobi ya nuna kyakkyawar hadin-gwiwa tsakanin Sin da Kenya
2017-06-01 10:50:34 cri

A jiya Laraba 31 ga watan Mayu ne, aka kaddamar da babban layin dogo daga birnin Mombasa zuwa birnin Nairobin Kenya wanda wani kamfanin kasar Sin ya gina. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Zhang Ming ya bayyana cewa, kaddamar da wannan muhimmin layin dogo, ya nuna cewa, akwai kyakkyawar hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin Sin da Kenya.

Mista Zhang ya ce, duba da yadda ma'aikatan kasashen biyu suka yi kokari, shekaru biyu da rabi kawai aka kwashe wajen aikin ginin wannan layin dogon, lamarin da ya shaida cewa kasar Sin na iya gudanar da aikin gine-gine masu inganci kuma cikin sauri.

Mista Zhang ya ce, layin dogon da aka kaddamar tsakanin Mombasa da Nairobi, wata babbar nasara ce ta manyan shirye-shirye guda goma na hadin-gwiwar Sin da Afirka, wadanda aka sanar da su a yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wanda aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Kana, wannan layin dogon ya kasance wata muhimmiyar alama ta hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskar zirga-zirgar jiragen kasa da masana'antu, kana wata sabuwar nasara ce da aka samu wajen aiwatar da shawarar 'ziri daya hanya daya' tsakanin Sin da Afirka.

Mista Zhang Ming ya kara da cewar, layin dogon da aka kaddamar tsakanin Mombasa da Nairobi, wani muhimmin bangare ne cikin tsarin zirga-zirgar jiragen kasa a yankunan gabashin Afirka, abun dake da muhimmiyar ma'ana ga raya tatttalin arziki gami da kyautata zaman rayuwar al'umma a kasar Kenya, da kuma kara habaka mu'amala tsakanin kasashen gabashin Afirka, da raya masana'antu a nahiyar ta Afirka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China