in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na fatan kara yawan cinikayya tsakanin kasashen Afirka nan da shekara 2021
2017-06-30 20:28:41 cri
Kungiyar tarayyar Afirka wato AU a takaice tana kokarin bullo da matakai da nufin ninka yawan cinikayya tsakanin kasashen dake nahiyar zuwa kaso 28 cikin 100 nan da shekara 2021.

Kwamishinan kungiyar ta AU mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu Muchaga Albert wanda ya bayyana hakan, ya ce kungiyar na fatan cimma wannan buri karkashin shirin nan na yankin cinikayya cikin 'yanci ko CFTA.

Kungiyar ta hannun shirin na CFTA suna shirin bullo da kasuwar hajoji da hidimomi ta bai daya, wadda za ta rika saukaka zirga-zirgar 'yan kasuwa da masu zuba jari.

Albert ya kuma shaidawa manema labarai yayin taron kolin kungiyar AU karo na 29 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cewa, shirin na CFTA ya hada kan kasashen Afirka 54 masu yawan al'umma sama da miliyan 1 da ma'aunin GDP da ya kai sama da dala triliyan 3.4

A shekarar 2015 ne shugabannin Afirka suka kaddamar da shirin na CFTA yayin taron kolin kungiyar AU da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China