Ana saran taron wakilan ya shirya ajandar taron kolin kungiyar inda za a gabatar da shawarwarin da ake fatan hukumar zartarwar kungiyar za ta amince da su, yayin zamanta a ranar 30 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli, sai kuma taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar wanda zai gudana daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Yuli.
A cewar shugaban hukumar zartarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat, taron kolin AU na bana zai mayar da hankali kan batutuwan zaman lafiya da tsaro da batun kaurar jama'a a nahiyar da sauransu. Sauran sun hada da abubuwan dake faruwa a kasashen Sudan ta kudu, Libya, Mali, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Burundi, Jamhuriyar demokiradiyar Congo, da yankin Darfur da Somaiya da sauran muhimman batutuwa.
Taron kolin na bana dai zai gudana ne daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yuli.(Ibrahim)