in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta gudanar da wani taron masana kan yaduwar kananan makamai ba bisa ka'ida ba a Afrika
2017-06-17 13:03:01 cri
Hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika da hadin gwiwar cibiyar da ke bincike da tattara bayanai kan batutuwan da suka shafi kananan makamai, sun shirya wani taro dake da nufin datse yaduwar haramatattun makamai a nahiyar Afrika.

Sanarwar da Kungiyar AU ta fitar a jiya Jumma'a ta ruwaito cewa, taron na yini biyu da ya gudana a ranakun 13 da 14 ga watan nan a hedkwatar Tarayyar Afrika dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya samu halartar masana daga kungiyoyin raya yankunan Afrika daban daban da hukumomin MDD da masu bincike.

Ana gudanar da binciken na gano yadda makaman ke yaduwa ne karkashin jadawalin taron kwamitin sulhu da wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU da ya gudana ranar 24 ga watan Afrilun 2014 mai taken 'kawar da bindigogi, tubalin wanzar da zaman lafiya a Afrika ya zuwa shekarar 2020", wanda ya nemi hukumar ta AU ta yi nazari kan yadda haramtattun makamai ke shiga da yaduwa a cikin nahiyar, sannan ta mika sakamakon binciken.

Wannan shi zai ba AU da kungiyoyin raya yankuna da kasashe mambobi su kare yaduwar haramtattun makamai zuwa yankunan dake fama da rikici, da aiwatar da dabaru da matakai da za su dace da manufofin kungiyar AU na kawar da bindigogi a nahiyar kawo shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China