A yayin ganawar ta su, Xu ya ce, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar kasar Kongo Kinshasa, da karfafa hadin gwiwa irinta moriyar juna a fannonin samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da fannin hakar ma'adinai da makamashi, da raya al'adun bil'adam da sauransu, duka dai da zummar samar da kuzari ga dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare irinta moriyar juna tsakanin Sin da kasar Kongo Kinshasa.(Fatima)




