Gwamnan jihar North Kivu ya bayyana cewa, baki daya fursunoni 930 ne suka tsere, yayin da masu kula da gidan kurkuku 8 da masu kai harin 3 suka mutu. Ya ce, masu kai hari sun yi amfani da manyan makamai.
Kawo yanzu, ba a gabatar da cikakken rahoto dangane da masu kai harin ba. Bisa labarin da hukumar tsaro ta bayar, an ce, masu adawa da gwamnatin Uganda da masu dauke da makamai farar hula na yankin ne suka aikata wannan danyen aiki.
An labarta cewa, mafi yawan fursunonin da suka tsere daga gidan kurkuku membobi ne na wadannan kungiyoyi biyu. Ana tuhumar su ne da laifin kisan kiyashi kan fararen hula a yankin, har ma wasu ana shari'arsu a halin yanzu. (Fatima Liu)