in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya kalubalanci Kongo Kinshasa da ta bincike kan matsalar kisan fararen hula
2016-08-17 13:40:29 cri

Kwamitin sulhun MDD, ya ba da wata sanarwa a jiya Talata 16 ga wata, inda ya yi Allah wadai da kisan fararen hula da 'yan fafutuka suka yi a wani kauye dake kasar Kongo Kinshasa, ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar da ta yi cikakken bincike kan wannan matsala, tare da daukar karin matakan kawar da illar da kungiyoyi masu dauke da makamai ke haifar.

Wani jami'in kasar Kongo Kinshasa ya bayyana a ran 14 ga wata cewa, 'yan adawa masu fafutuka a Uganda, sun kai hari kan wani kauye dake gabashin kasar a daren ranar 13 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 45. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China