A cikin sanarwar, an ce daga rana 19 zuwa ta 20 ga wata, an tayar da rikice-rikicen nuna karfin tuwo tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a birnin Kinshasa da sauran wurare, wadanda suka haddasa rasuwar mutane a kalla 32, ciki har da 'yan sanda guda hudu, dalilin haka, kwamitin sulhu yake nuna damuwa sosai kan lamuran tare da yin allawadai sosai kan miyagun ayyukan da aka yi.
Baya ga haka, kwamitin sulhu ya yi kira ga jam'iyyu daban daban na kasar Kongo Kinshasa da masu goyon bayansu da su dakatar da ayyukan nuna karfin tuwo da na harzuka, tare kuma da kawar da bambance-bambance a tsakaninsu ta hanyar lumana, kana ya kalubalanci jam'iyyu daban daban na kasar da su yi hakuri da hana daukar matakan da za su kara tsanantar da hali, ya kuma kalubalanci gwamnatin kasar da ta yi bincike tare da gurfanar da masu hannu cikin wadannan munanan ayyukan gaban kotu.
A karshe dai kwamitin sulhu ya kara yin kira ga bangarori daban daban na kasar, da su shirya wata tattaunawar siyasa game da batun shirya zaben shugaban kasar yadda ya kamata. (Bilkisu)