in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Kongo Kinshasa ya mika sakon murabus zuwa shugaban kasar
2016-11-15 11:01:52 cri
A jiya Litinin 14 ga wata, firaministan Kongo Kinshasa Augustin Matata Ponyo Mapon, ya shelantawa kafofin yada labarai cewa, ya riga ya mika takardar murabus zuwa shugaban kasar Joseph Kabila. Ya ce hakan na da nasaba da yarjejeniyar hawa teburin shawarwarin siyasa.

A ranar 18 ga watan Oktobar da ya gabata ne dai bangaren mafiya yawan ma'aikatan gwamnati, da na 'yan adawa da gwamnati, suka rattaba hannu kan yarjejeniya bayan shawarwarin da suka yi game da babban zaben kasa, da mika mulkin kasa. Bisa yarjejeniyar, dole ne a nada sabon firaministan kasar cikin gaggawa, kana a kafa sabuwar gwamnatin cikin hanzari.

An dai jinkirta babban zaben kasar Kongo Kinshasa zuwa watan Afrilu na shekarar 2018. Bayan cikar wa'adin aikinsa a karshen shekarar nan, shugaba Joseph Kabila Kabange, zai ci gaba da aiki ya zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaban kasar.

A baya dai an tsara gudanar da zaben shugaban kasar Kongo Kinshasa a ranar 20 ga watan Satumbar bana, amma kwamitin zaben kasar ya nace cewa, sai an sabunta sunayen masu jefa kuri'a tukuna, don haka dole a jinkirta babban zaben kasar. Sai dai a hannu guda bangaren 'yan adawar kasar ya nuna rashin amincewa da wannan mataki.

Tsakanin ranekun 19 zuwa 20 ga watan Satumba, 'yan adawa sun yi zanga zanga a birnin Kinshasa, hedkwatar kasar. Wannan mataki ya haifar da rikicin zubar da jini tsakanin masu zanga zanga da sojoji, da kuma 'yan sanda, yayin da wasu mutane 32 suka mutu a sakamakon tarzomar.(Fatima)

  

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China