in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici na cigaba da tsananta a Kinshasa
2016-09-21 13:01:37 cri
Riciki na cigaba da tsananta a birnin Kinshasa na kasar Kongo Kinshasa tun bayan aka tada wuta a hedkwatar jam'iyyar adawa mafi girma, a ranar jiya 20 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 3.

An ba da labari cewa, a daren ran 19 ga wata, an sanya wuta a hedkwatar jam'iyyar Union for Democracy and Social Progress, babbar jam'iyyar adawa a kasar, a sassafen ranar 20 ga wata kuma, an gano gawawaki mutane 3 a wurin, yayin da wasu 2 suka tsananin raunuka.

Bisa labarin da aka bayar an ce, tun daga ran 19 ga wata, kantunan Sinawa fiye da 10 sun nemo ceto saboda masu zanga zanga sun kewayensu. Ya zuwa yanzu Sinawa fiye da 100 ne aka kai su zuwa wurin da ya fi kwanciyar hankali karkashin taimakon da kungiyoyin Sinawa dake kasar, amma an yi ta kwasar ganima kan kantunansu. An kuma bayyana cewa, Sinawa a kalla 200 da ba su kaura daga wurarensu ba suna cikin mawuyacin hali.

Masu adawa na kasar Kongo Kinshasa sun yi zanga-zanga a ran 19 ga wata a birnin Kinshasa domin nemo gwamnatin da ta gudanar da zabe cikin daidai lokaci, duban masu zanga-zanga sun yi fito-na-fito da 'yan sandan kasar, lamarin da ya halaka mutane da dama.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar, Kongo Kinshasa za ta gudanar da zaben shugaban kasar a ran 20 ga wata, amma kwamitin zabe yana ganin cewa, ya kamata an kyautata takardun masu kada kuri'u da farko, hakan ya sa dole ne aka tsawaita lokacin zabe, hakan ya haifar da zanga-zanga da rashin jin dadi dsaga wajen masu adawa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China