Liu wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a yayin taron da ya gudana daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Mayun wannan shekara, ya ce akwai bukatar yin aiki tare ta yadda kasashen Afirka za su hade tsarin makamashinsu da na sadarwa waje guda, kana su kara ba da gudummawa don samar da ci gaba mai dorewa.
Ya kuma bayyana cewa, hukumarsa a shirya take ta hada kai da kasashen Afirka ta hanyar mutunta juna da samun moriya tare, a wani mataki na inganta tsarin makamashin nahiyar.
A nasa jawabin firaministan kasar Habasha, Hailemariam Desalegn, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don zakulo hanyoyin samar da makamashi mai dorewa ta yadda za a farfado da tattalin arzikin kasashen nahiyar.
Wani rahoto game da matsayin makamashi bisa karfin ruwa na shekarar 2017 da aka fitar, ya nuna cewa, nahiyar Afirka ce ke kurar baya a bangaren makamashi, musamman kasashen da ke yankin kudu da hamadar Sahara, lamarin da ke kawo nakasu ga ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a a shiyyar.
Rahoton wanda kungiyar kula da harkokin makamashi bisa karfin ruwa ta duniya ta fitar, ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu sama da kasashen Afirka 30 ne suke fama da karancin wutar lantarki, lamarin da ya haifar da yawan dauke wutar da yadda ake dogaro a kan wutar duk da tsadarta, matakin da a wasu lokuta kan haifar da illa ga muhalli.(Ibrahim)