in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 19 a wani fadan kabilanci a yankin Darfur na kasar Sudan
2017-04-30 13:07:05 cri
Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, a kalla mutane 19 ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 19 kuma suka jikkata, sakamakon wani fadan kabilanci da ya barke a yankin Darfur na kasar Sudan.

Jaridar Sudan Tribune ta ba da rahoton cewa, fadan ya barke ne bayan da wasu mutane dauke da makamai 'yan kabilar Salamat suka yi awon gaba da shanu na 'yan kabilar Habaniya.

An ruwaito wani jami'in yankin yana cewa,an tura sojoji don raba sassan biyu tare kuma da hana aukuwar fadan a nan gaba.

Bayanai na cewa, tsawon shekarun da aka dauka ana kokarin kawo karshen fadan kabilanci a yankin ya ci tura, lamarin da ke haifar da damuwa ga mazauna da ma hukumomin yankin dake fama da tashin hankali.

Matsalolin tsaro da yadda kabilun yanki ke rike da makamai da rashin kyakkyawan shugabanci a galibin yankunan dake shiyyar, suna daga cikin abubuwan dake haddasa tashin hankali a yankin na Darfur.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China