Wani mai magana da yawun jihar West Darfur ya yi bayani kan abun da ya faru ga wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ta wayar tarho, inda ya ce al'amarin sace mutanen ya abku ne a yammacin ranar Lahadi bisa agogon wurin. A cewarsa, wasu dakaru sun kutsa kai cikin ofishin hukumar UNHCR dake garin Geneina, tare da yin awon gaba da ma'aikatan ofishin 3, sa'an nan suka bar wurin cikin motoci.
An ce yanzu haka jami'an tsaron jihar West Darfur suna kokarin bincike kan dakarun da suke da alhakin aikata wannan danyen aiki, kuma a shirye suke don kubutar da mutanen da aka sace, duk lokacin da aka tabbatar da wurin da ake tsare da su. (Bello Wang)