in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAMID ya ce amfani da karfin soji ba zai shawo kan rikicin Dafur ba
2016-12-29 10:25:07 cri
A jiya Laraba ne shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin MDD da Tarayyar Afrika UNAMID, dake aiki a Dafur, ya ce amfani da karfin soji ba zai shawo kan rikicin da ake yi ba.

Da yake jaddada wannan batu cikin sakonsa na karshen shekara, shugaban shirin na UNAMID Martin Uhomoibhi, ya ce suna ci gaba da kokarin warware rikicin tare da wanzar da zaman lafiya.

Ya ce shirin zai ci gaba da kokarin sauke nauyin dake wuyansa, tare da jajircewa wajen wanzar da zaman lafiya da samar da tsaro a Dafur.

Rikici tsakanin al'ummomi daban-daban a Dafur, da wata sabuwar fitina da ta kunno kai a yankin Jebel Marra, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama tare da raba wasu da yawa da matsugunansu.

Ya kara da cewa, al'ummar Darfur da ma'aikatan UNAMID sun fuskanci kalubale da dama a wannan shekarar, yana mai bada misali da mutuwar jami'in shirin dan asalin kasar Afirka ta Kudu da ma wasu da suka rasa rayukansu ya yin rikice- rikicen.

Shirin UNAMID ya kunshi jami'an soji da 'yan sanda da fararen hula sama da dubu ashirin, inda ya karbi aikin wanzar da zaman lafiya a Darfur daga hannun Tarayyar Afrika a ranar 31 ga watan Disamban 2007.

Ana kuma kallon shirin a matsayin shirin wanzar da zaman lafiya mafi girma a duniya, baya ga wanda MDD ke yi a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. (Faiza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China