A jiya Alhamis ne majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka suka ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi tir da harin da 'yan tawaye suka kai kan sansanonin mutanen da suka rasa muhallinsu dake kusa da wata kasuwa a yankin Darfur na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, yayin da wasu suka jikkata. (Tasallah Yuan)