Liu Jieyi wanda ke jawabi yayin taron kwamitin sulhun MDD, ya ce kamata ya yi kasashen duniya su ci gaba da nuna goyon baya, ga aikin shiga-tsakani da rukunin gudanarwar kungiyar AU ke gudanarwa, da gaggauta taimakawa gwamnatin kasar Sudan, wajen cimma yarjejeniya a tsakaninta da tawagar dakaru da masu adawa.
Sauran matakan sun hada da warware matsaloli ta hanyar gudanar da shawarwari, da neman warware batun yankin Darfur cikin lumana. Kana yana fatan bangarori masu bada gudummawa, za su cika alkawarinsu na samar da gudummawa, da taimakawa gwamnatin kasar Sudan, wajen gina ababen more rayuwa, da inganta karfin samun bunkasuwa a yankin Darfur, don samar da ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'umma mai dorewa a yankin. (Zainab Zhang)