Yadda Moody's ya nuna raunin tattalin arzikin kasar Sin bai dace ba, in ji ma'aikatar harkokin kudi ta kasar
A yau Laraba ne, hukumar dake kimanta karfin tattalin arziki na kasa da kasa, wato Moody's ta rage matsayin tattalin arzikin kasar Sin da mataki guda, wato daga Aa3 zuwa A1. A game da wannan, ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin ta ce, hanyar da hukumar ta bi wajen kimanta tattalin arzikin kasar Sin ba ta dace ba, musamman ma yadda take ganin basussukan da kasar ta ci za su karu da sauri kuma da wuya hakarta ta cimma ruwa a matakan da ta dauka na yin kwaskwarima, a cewar ma'aikatar, yadda hukumar Moody's ta kiyasta matsalolin da tattalin arzikin kasar Sin ke fuskanta sun wuce kima, kuma ba ta fahimci kwarewar gwamnatin kasar ta fannin yin gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki da kuma habaka bukatu ba. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku